TUKI ALOKACIN MATSALA
A baya munyi bayani game da dabarun tuki akan titi da kuma,
dabarun tuki a wasu lokuta na musamman.
Yau za mu yi bayanine game da yadda mutum ya kamata ya sarrafa motarsa,
alokacin da wata matsala ta afku yayin da yake tuki.
Asha karatu lafiya.
1.
TUKI ALOKACIN ZAMEWAR TAYA
A wasu lokutan, musammanma alokacin da ake
ruwan sama ko kuma, akan titin da ke da tsakuwoyi , ko kuma alokacin da direba
katsam ya taka birki ko ya juya sitiyari,
tayar mota kan iya rasa kamawar da take yiwa titi saboda santsi. Wannan
kan iya sanyawa taya ko tayoyi su zame wanda hakan ka iya sanya direba ya rasa
damar sarrafa motar. Wannan yanayi ka iya janyo hatsari da zai iya sanya asarar
rayuka. Allah ya kyauta.
Akwai abinda direba ya kamata ya yi domin
kare afkuwar hatsari alokacin faruwar zamewar taya ko tayoyin mota.
Abin da kan faru idan tayoyin gabane suka
zame shine; motar zata mikene sosai a maimakon take bin juyawar sitiyari. Idan
zamewar tayar ya farune saboda taka birki katsam, to sai ka dan sassauta ka
taka birki a natse ka kuma tsaida kan motar (wato sitiyari). Idan kuma zamewar
tayar ya farune saboda gudu mai yawa (wayaga fanfalaki), sai kai maza ka cire
kafarka daga kan totir sannan ka tsai da kan motar ka kuma taka birki ahankali.
Abin kuma da kan faru idan tayoyin bayane
suka zame shine; motar zata fizgekane gefe.
Idan hakan ta faru, saika juya sitiyari a
natse domin ka dawo da motar yadda ya kamata. Kada ka firgita har ka juya
sitiyarin ya wuce yadda ya kamata. Juya sitiyarin fiye da yadda ya kamata ka
iya jawowa motar ta yi yawo wadda hakan na da matukar hatsari. Ka tabbata ba ka
taka totirba har zuwa lokacin da ka sami kan motar!
2.
TUKI ALOKACIN FASHEWAR TAYA
Idan taya ta fashe mota kan fizgi
direbane zuwa wani bangare. Idan hakan
ta faru sai mutum ya taka birki ahankali kuma, a natse sannan ya rike sitiyari
da karfi ya nemi wurin da zai tsaya a gefen titi. Taka birki da karfi na da
matukar hatsari a irin wannan yanayi!
Kada mutum ya kuskura ya taka totir a irin wannan yanayi!
3.
TUKI ALOKACIN KWALEWAR BIRKI
Hausawa kan ce “karfen nasara baka da
tabbas”. Wannan haka yake. Akwai wasu lokuta da birki kan yiwa direba bazata.
Idan irin wannan bazata ta faru wato, katsam birki ya kwale kana cikin zura
gudu, yaya zakayi?
Idan birkinka yakwale ana so kake taka
birkin kana dagawa da sauri da sauri abin da ake kira a turance ‘pumping’,
sannan ka canja giyar motar zuwa babbar giya, sai kuma ka ja birkin ajiye mota
(parking brake). Idan kana tsoron tsayawa akan titi saboda ragas sai ka bar kan
titin. Ka tuna idan yin ragas ya zama dole, sai ka durfafi wurin da kasan zai
fi maka sauki idan aka hadu!
Allah ya kyauta.
Tuki acikin ruwa kan rage karfin birki. An
so da ka fita daga cikin ruwan ka ke tafiya ahankali sannan kuma ka dora
kafarka akan birki ahankali zuwa dan wani lokaci, don birkin ya bushe.
4.
TUKI ALOKACIN RAGAS
Allah ya kyauta. Wataran akan sami yanayi
da kansa mota da mota su hadu da juna,
wato ayi ragas. Akwai wasu direbobin da duk yadda ka yi das u sai sun
janyo maka jangwam. Irin wadannan direbobin kan kasance kodai ‘yankwayane,
kokuma wadanda hanunsu bai fadaba kuma
suke jin sun wuce makala ‘L’ a motarsu. Da zasu makala ‘L’ din da sai ka gane cewa sabon
hanune kasan yadda za ka bi dasu.
Wasu direbobin da kan jawo ragas kuma
baccine yake daukarsu sannan kuma saboda wasu dalilai da, su suka sanma kansu,
ba za su tsaya su yi abin da zai tafi da baccin nasu ba kafin su dora akan
tafiyar tasu.
Wasu kuma kan jawo ragas ne saboda rashin
kula da gyaran motarsu, wasu kuma saboda rashin bin dokokin hanya dana tuki.
Ragas kan farune ta gaba da gaba ko ta gaba
da baya ko ta baya da baya (wadda keda wahalar afkuwa).
Idan ragas zai faru ta gaba da gaba, kada
ka firgita, kada kuma kai saurin juya sitiyari domin baka saniba ko daya
direbanma nan yake son ya juya. A maimakon haka sai ka kunna fitila ka kuma
danna ham domin fargar da direban. Bayan haka sai ka duba hagun dinka domin
ganin yiwuwar komawa bangaren. Idan
akwai bukatar tsayawa sai ka sauka daga kan titi ka tsaya.
Zai iya yiwuwa ayi ragas ta gaba da baya,
inda wani zai buga wa mota ta baya (wato abin da wasu ke kira; Karin gudu). A
irin wannan yanayi an so wanda aka bugawa din ya natsu ya kalli gefe da gefensa
don ganin ko akwai mota. Kada yai saurin taka birki. Zai rike kan sitiyarinsa
gam yadda zai kare kansa daga yawo sannan kada ya soma ya taka totir. Daga nan
sai ya nemi wurin da zai tsaya a kasan titi domin jiran abin da zai biyo baya.
Ya zama dole ga duk wanda ya ajiye mota a
gefen titi don faruwar wata matsala ya sanya alama akan titin domin nunawa mai
zuwa cewa akwai mota a wurin. Rashin yin haka kan haddasa hatsari a lokuta da
dama! Ni kaina ya taba jawo mani.
Allah yasa dan abin da muka fada ya
anfanar.
Sai mun hadu a batu na gaba.
Mai tambaya zai iya aiko mana ta akwatun
yanar gizonmu: zaurenmotoci@gmail.com
ko kuma ya rubuta a ‘comment box’ din wannan makala a kasa.
No comments:
Post a Comment