Wednesday, September 26, 2012

KALAR HAYAKIN MOTA: ME YA KE NUFI?


Mota mai hayaki
         
Kowacce mota tana fitar da hayaki ta wani kororon karfe da ake kira salansa (silencer). Ga mota mai cikakkyiyar lafiya, mutum ba ya iya ganin hayakin da idonsa.
A duk lokacin da ka ga mota na fitar da hayaki ta salansarta to akwai wani dalili.
Wannan dalili ya danganta ne ga kalar hayakin da motar ke fitarwa. Akan haka za mu gabatar da makalarmu ta yau.

1. FARIN HAYAKI MARAR DUHU

Ba abin damuwa bane idan ka ga motarka na fitar da farin hayaki marar duhu (wato shara-shara). Yawancin hakan kan farune farkon tayar da mota da safe, barinma idan yanayin gari ya kasance da sanyi-sanyi.

Wataranma ka kan ga salansar na dan digar ruwa.
Kamar yadda muka ce, farin hayaki shara-shara baya nuna cewa akwai matsala a injin mota. Sai ka sha kuruminka!

2. FARIN HAYAKI MAI DUHU

Babbar matsalace  idan ka ga mota na fitar da farin hayaki mai duhu. Wannan kan farune idan ya kasance ruwa na shiga cikin tukunyar gashi (engine cylinder) ta injin mota.
Abubuwan da ke kawo faruwar hakan sune; lalacewar taf silinda gaske (top cylinder gasket), ko lalacewar taf silinda (top cylinder) din kanta, ko kuma tsaguwa a bangon tukunyar gashi (engine cylinder).
Idan hakan ya faru dole ne  sai an kunce injin motar kafin a magance matsalar.
Yana da matukar mahimmanci da mutum ya ga motarsa na fitar da farin hayaki mai duhu, ya kashe motar sannan ya samo wani ya ja masa motar izuwa wurin mai gyara kwararre.

3. SHUDI-SHUDI KO TOKA-TOKAN HAYAKI MAI DUHU

Idan ka ga moatarka na fitar da shudi-shudi ko toka-tokan hayaki mai duhu to akwai matsala.
Abin da ke kawo irin wannan hayaki shine shigar bakin mai (engine oil) cikin tukunyar gashi (engine cylinder).
Wannan kan jawo ka ga bakin mai a injin motarka na saurin sauka ko raguwa. Sannan kum fulogi zai ke jan mai akai akai. Hakanan kuma idan abin ya yi kamari, za ka ga salansar motar na fitar da dussar hayaki mai laimar bakin mai.
A duk lokacin da ka ga motarka ta fara fitar da irin wannan hayaki, ya kamata ka garzaya da wuri, zuwa wurin mai gyara tun kafin abin ya ta'azzara, kilu ta jawo bau!

4. BAKIN HAYAKI

Fitar bakin hayaki daga salansar mota shima, na nuna cewa akwai matsala a motar.
Abin da ke sanya mota ta ke fitar da bakin hayaki shine, idan ana samun mai (man fetur) fiye da kima na shiga cikin tukunyar gashi (engine cylinder).
Abubuwan da ke sa hakan ta faru sune; dattin matatar iska (air cleaner), ko matsalar kafireto (carburetor), ko matsalar injesta (fuel injector), ko kuma matsalar masansanan mota (engine sensors).
Irin wannan matsalar kan kawo shan man fetur a mota da kuma wahalar tashi da dai 'yan sauran wasu matsalolinma.
Yana da kyau da ka ga motarka na fitar da irn wannan hayaki ka garzaya wurin mai gyara don ya duba maka.
WANNAN BAYANI AN YI SHI NE AKAN MOTA MAI AIKI DA MAN FETUR!
Da fatan 'yar wannan makala za ta amfanar.
Allah ya taimakemu, amin.

No comments:

Post a Comment