Wednesday, November 7, 2012

TATTALIN MAI A MOTA: YA AKE YI?


Toyota Pirius: daya daga cikin motocin da suka fi kowacce saukin shan mai a duniya.


A yau, man da mu ke zubawa motocinmu ya zama sai a hankali saboda, kasancewar yawan karancinsa da kuma tashin gwauron zabo da farashinsa kan yi.
Saboda dalilan da na zayyana a sama naga, ya kamata na yima mutanen da ke bibiyanmu bayani, game da yadda za su rage shan man fetur ko gas da motarsu kan yi.
A sha karatu lafiya.

1.       Sayen mota mara shan mai. Wasu motocin sun fi wasu rashin shan mai.
2.       Duba lafiyar mota akai akai. Bada kulawa ga matatar iska (air filter) da (fulogai) da  kuma layin mai  a mota na da matukar mahimmanci wurin rage shan mai a motar.
3.       Yin tafiya a lokacin da babu cunkoso a titi.
4.       Lura da yanayin tayoyin mota. Rashin isashshiyar iska a tayoyi na jawo shan mai a mota. Bashi da kyau kuma mutum ya sanya iska ta yi yawa a tayoyin motarsa. Sai a lura! Sayan tayoyi masu kyau na taimakawa wurin rage shan mai a mota. Akwai abin da ake kira ‘rolling resistance’. Tayar da take da karanci ‘rolling resistance’ kan taimaka wurin rage shan mai.
5.       Tayoyi masu fadi sun fi marasa fadi kawo shan mai
6.       Sayan mai a gidan mai mai farashi da sauki sannan kuma man nasu ya kasance mai kyau. Ka lura sosai wurin barin hanya don neman mai mai suki domin kuwa idan ka sake sai araha ta kasa yin ado!
7.       Tsara tafiyarka yadda ba zai kasance aje a dawoba. Ka kuma shirya tafiyar taka ta yadda zai kasance ka sami cikakkyen amfaninta. Kada a yi tafiyar da sai an dawo a tuna cewa ba ayi kaza ba, yadda zai kasance sai an koma.
8.       Yi gudu a matsakaiciyar tafiya. Yin tafiya a casa’in (90km/hr) zai rage maka shan mai akan yin tafiya a dari da ashirin (120km/hr). Yin tafiya bai daya na rage shan mai matuka. Abin da na ke nufi bai daya shine, kamar ka tafi a casa’in (90km/hr) ba canji.
9.       Kada ka dora kaya a saman motarka sai idan har ba yadda za ka yi. Dora kaya a saman mota na jawo karuwar shan mai.
10.   Yawan kaya ko mutane a cikin mota na jawo karuwar shan mai
11.   Tabbatar da ka rufe tankin motarka dai dai
12.   Kiyayi barin motarka tana yin sulo (idle) na ba gaira ba dalili
13.   Yin amfani da na’urar sanyaya mota ‘car AC’ idan ana gudu a mota ya fi akan abar gilasai a bude. Amma idan ana tafiya a hankali barin gilasai a bude  ya fi akan a kunna na’urar sanyaya motar.
14.   Bincike ya nuna cewa mota mara kulochi wato ‘Auto’ tafi  mota mai kulochi wato ‘manual’ shan mai. To fa!
15.   Kada ka tuka motarka haka kawai, sai dai in har kana da abin yi. Yi tunanin shiga motar haya ko babur ko kuma ma keke ko taka sayyada, kafin ka hau motarka
Karshen 'yar wannan makalar ke nan. Idan ana da tambaya sai a rubuta a comment box da ke kasan wannan makalar a rubuta.
SSai mun hadu a batu na gaba
Kada a manta, a yi Like din mu
Mun gode






No comments:

Post a Comment