Sunday, July 8, 2012

KULAWA DA MOTOCI: YA KA KE YIWA TAKA?

Mota, ko ta shiga, ko ta daukar kaya, ko ta diban mutane da yawa, na da bukatar kulawa ta musamman domin jin dadin tafiyar da ita da ma kuma daukar dogon lokaci ana amfani da ita, ba tare da ta lalaceba.

Abu mai mahimmanci ga mai mota shine, da ya ji dan wani motsi ko wata kara ko wani yanayi da bai saba ji a motarsaba to ya tuntubi mai gyara ,wato makanike (automechanic) don ya duba masa. Yin hakan da wuri zai iya rage masa kashe kudi mai yawa da zai iya faruwa idan ahankali kilu ta jawo bau wato, karamin gyara ya jawo babba.

Wajen zuwa wurin makanike kuma, abu ne mai mahimmanci ka sami wanda ya kware sosai. Samun wanda bai kwareba zai iya jawowa a yi maka aikin baban giwa ko kuma aikin jeka ka dawo. Lokuta da yawa masu gyara da basu kwareba ko kuma wadanda ake kira ‘yan gyara samun sa’a, sukan jawowa masu mota asara mai yawa, barinma masu aikin daya shafi bangaren wuta. Ni kaina na sha fuskantar irin wannan, musammanma a Abuja.

Yana da kyau kafin ka sami mai gyara ka bincika wurin daya kamata domin ka san irin kwarewarsa. Duk mai gyaran da ka ji ya fiya ziga kansa to ka ji tsoronsa domin kuwa Hausawa sunce; gwangwanin da babu komai cikinsa ya fi kara. Ban kumafa ce duk mai gyaran motar da bai fiya surutuba kwararrene. Sai ayi hattara!

ABUBUWAN DA YA KAMATA KAKE YI GAME DA MOTARKA

Idan har ka jure yin abubuwan da zamu zayyana maka a kasa, motarka za ta dau lokaci mai tsawo kana jin dadinta in Allah ya yarda.

1)      Ka ke duba bakin mai (engine oil) akai akai. Yana da kyau mai mota yake canza bakin man motarsa duk bayan ya cinye kilomita kimanin dubu biyar (5,000Km). Wasu za ka ga suna amfani da kwanaki ko watanni domin canza bakin man motarsu; wannan ba shine abin da ya kamataba. Idan ba ka fiya hawan motarka ba har ka yi wata uku ba ka cinye kilomita dubu biyar (5,000Km) ba to sai ka canza bakin man a dai dai wata uku. Ana kuma son ka ke canza filtar bakin man (oil filter) a duk bayan cinye kilomita dubu goma (10,000Km), wato kimanin canjin bakin mai biyu.

2)      Ka ke duba tayoyin motarka akai akai domin tabbatar da kyawunsu da kuma cikar iskarsu. Ka tabbata kodayaushe suna a geji (guage). Idan iska tai yawa a taya, tayar kan sude ta tsakiyarta; idan kuma iska bata kaiba, taya kan sude a gefe da gefenta. Sudewar taya a gefe guda kadai na faruwane yawanci saboda matsalar alamin (wheel alignment) ko kuma guga.

3)      Ka ke duba ruwan birki (brake fluid) akai akai. Rashin isashshen ruwan birki na kawo matsalar iska ta shiga layin birki (brake circuit) inda hakan kan kawo rashin jin birki a mota, wato kwalewar birki. Kowa dai ya san mahimmancin birki a mota. Wa ya ga zura ka hau!

4)      Duba kafar batiri (battery terminals) akai akai. Idan sun yi tsatsa sai a wanke ko a kankare a hankali sannan a mayar da wayoyin. Bayan mayar da wayoyin sai a sanya basilin (vaseline) wanda yin hakan zai kare su daga yin tsatsar. Tsatsar kafar batiri kan janyo wuyar tashin mota.

5)      Duba man giyabos (gearbox) da na kundu (differential) daga lokaci zuwa lokaci (kamar duk bayan wata uku).

6)      Duba man sitiyari (power steering oil) daga lokaci zuwa lokaci (kamar duk bayan wata uku).

7)      Duba alamin din kafofin mota (wheel alignment). Rashin alamin kan jawo mutuwar tayoyi da wuri da kuma yawo akan titi sannan da taurin sitiyari.

8)      Duba matatar iska (air filter) daga lokaci zuwa lokaci. Yawan shiga cikin kura kan sa matatar iskar mota ta ke yin datti da wuri. Daga cikin illar dattin matatar iska shine mota ta ke shan mai. Kowa dai ya san tsadar mai a wannan zamani. Ya kamata ake duba matatar iska a bayan cinye tafiyar kilomita dubu goma sha biyar (15,000Km).

9)      Duba matatar mai (fuel filter) daga lokaci zuwa lokaci. Yin dattin matatar mai kan sanya wahalar tashin mota da kuma jijjiga idan ana cikin tafiya ko kuma idan za a daga.

10)   Duba lagireta (radiator) akai akai domin tabbatar da cewa akwai ruwa isashsha a cikinsa. Rashin ruwa a lagireta na da hatsarin gaske ga injin mota. Akwai bukatar kuma ake tabbatar da cewa lagireta bashi da datti akodayaushe. Yin dattin lagireta kan jawo inji yake yin zafi sosai wanda hakan na da illa ga injin mota. Kar a zubawa lagireto ruwan sanyi a lokacin da inji yake da zafi. Yin hakan na iya jawo tsagewar injin mota. Ka dan jira inji ya yi sanya kafin ka yi Karin ruwa a lagireta.

11)   Ka tabbatar ka sanar da masu wanke maka mota cewa su tabbatar da ruwa bai shiga matatar iskar motarka ba (air filter). Sannan kuma su tabbatar da ruwa bai taba duk wani abu mai aiki da wutar lantarki a motarba. (Rashin fadakar da mai mani wankin mota game da wannan sai da ya janyo mani asarar naira dubu shida (N6,000), banda asarar lokaci)

12)   Canja fulogai (spark plugs) bayan cinye kilomita dubu goma (10,000Km).

13)   Ka ke kai motarka a yi mata binciken kwakwaf bayan duk shekaru uku.

A karshe, idan zaka sayi kayan gyaran motarka, ko duk wani abu don motarka, ka tabbata ka sayi mai kyau.

Da fatan wannan dan takaitaccen bayani zai amfanar.

Sai mun hadu a batu na gaba.

No comments:

Post a Comment