Wednesday, July 11, 2012

DABARUN TUKI AKAN TITI



Yau zamu yi iya kokarinmu ne wurin sanar da ku yadda ya kamata direba ya tuka motarsa. Mun sami wannan bayanine ta yin bincike ta hanyar tuntubar kwararru da kuma yin amfani da dan abinda muka sani  ta hanyar yin tukin da kanmu da kuma ta yin mu’amala da matuka motocin.

 Muje Zuwa:

Babban abu na farko da ake so ga direba shine cikakkiyar lafiya ta kowanne fanni da kuma natsuwa.

1.      Abu na farko da direba zai yi kafin ya fara shiga mota don yin tafiya shine duba lafiyar motar tasa. Ya zama wajibi ga direban ya duba fitulun motar (lights) da birki (brakes) da tayoyi (tyres) da abin share gilashin motar (windscreen wipers). Yana da matukar mahimmanci direba ya tabbatar cewa wadannan abubuwa da muka lissafa za su yi aiki kamar yadda ya kamata. Sannan wajibine  ga direba ya duba bakinman motarsa (engine oil) domin tabbatar da cewa yana geji (guage), sannan kuma ya duba lafiyar batirin motar da yawan man da ke cikin tankin motar da ruwan da ke cikin lagireto da man birki da kuma man sitiyari (ga mota ma abin da ake kira ‘power steering’). Yana kuma da matukar mahimmanci ga direba ya duba kasan mota da gabanta da kuma bayanta domin tabbatar da cewa ba wani abu da zai hau ta kansa ko kuma zai buga a lokacin daya fara tafiya da motar.

2.       Idan mutum ya shiga motar, ya kamata ya saita mirukan da yake amfani da su don kallon baya a lokacin tuki (rear view mirrors). Sannan yana da kyau ya waiga baya da kubi-da-kubi domin tabbatar daba wani abu da zai iya mangara idan ya fara tafiya da motar. Kafin direba ya fara tafiya yana da matukar mahimmanci ya nuna bangaren da zai nufa ta hanyar sanya signan (signal) din bangaren da zai nufa. Idan kuma zai mikene to ba sai ya kunna wata signa ba. Yana da matukar mahimmanci ya danna ham don sanar da cewa zai fara tafiya.

3.       Idan mutum ya hau kan titi lallaine ya bi bangaren dama a kodayaushe, sai dai in har zai wuce wanine. Bai kamataba ga direba ya ke bin tsakiyar titi. Mai bin titi mai hanu biyu (da na tafiya da na dawowa) yana da mahimmanci ya ke bin hannun damarsa in har ba gudu yake yi ba.

4.       Wajibi ne ga direba yake amfani da signoni domin nunawa mai binsa da wanda ke gabansa a duk lokacin da zai yanka bangaren dama ko kuma hagu. Yakamata direba ya tabbatar da cewa fitilar birkinsa na aiki domin baiwa na gabansa dama na bayansa sako a duk lokacin da ya taka birkin, wanda yin hakan zai taimaka masu su san yadda za su yi da motarsu don kare yin ragas.

5.       Yana da kyau direba yake tafiya yadda zai iya sarrafa motarsa koda ya yi kicibis da wani abu a gabansa. Yana da kyau mutum ya yi amfani da babbar giya idan ya tarar da hawa ko gangara. Anan muna nufin babban hawa ko babbar gangara.

6.       Yana da matukar mahimmanci direba yake barin ‘yartazara tsakaninsa da wanda ke gabansa. A dan wani kiyasi da muka yi, yana da kyau ace zaka iya cewa, da karfi: daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida! kafin ka je wurin da direban da ke gabanka yake, a dai-dai lokacin da ka fara kirgar. Idan ka wuce wurin ba ka kammala kirgarba to sai ka rage gudu, domin kuwa gudun naka ya yi yawa!

7.       Yana da kyau direba yake shiga kwana cikin nutsuwa. Sannan yana da kyau direba ya nutsu sosai wurin dunfarar mahadar titi.

8.       Kada ka wuce mota har sai ka tabbatar zaka iya wuceta ba tare da wata matsalaba. Yana da matukar mahimmanci ka duba miro domin ganin yanayin bayanka. Dole ne ka danna ham ko kuma ka kunna fitala domin nunawa direban da za ka wuce aniyarka ta wuce shin. Sannan dole ne ka kunna signa don nunawa direban da ke bayanka da kuma direban da zaka wuce ta bangaren da zaka yanka. Ka kuma tabbata ka wuce motar da za ka tserewa kafin ka yanka gabansa.

9.       Ka tabbata ba wani abu a bayanka kafin ka yi baya da mota. Yana da kyau ka sami wani ya duba maka idan zaka yi baya da mota, sai dai in har ka tabbatar ba wata matsala.

Da fatan dan wannan takaitaccen bayanin da muka yi zai anfanar.

Sai mun hadu a batu na gaba in Allah ya yarda.

A cigaba da tayamu da addu’a.

No comments:

Post a Comment