Tuesday, July 17, 2012

DABARUN TUKI A WASU YANAYI NA MUSAMMAN

Tukin mota wani abune da ke da bukatar natsuwa a kodayaushe; akwai wasu lokutama da mutum ya kamata ya kara akan natsuwar tasa don magance yin ragas, ko kauce hanya, ko kumama hantsilawa.

Ayau zamuyi bayani ne akan yanayin tukin da mutum ya kamata ya yi idan ya sami kansa a wasu yanayi na musamman.

A sha karatu lafiya.


  1. TUKI A CIKIN RINTSI

     

    Akwai lokacin da direba zai iya samun kansa a cikin rintsin motoci, a gaba da baya da ma kuma gefe da gefensa. Irin wannan kan faru ne yawancin idan mutum yana tuki a cikingari. A irin wannan yanayi, ana son direba ya ke yin tukin da ake kira; tukin kare kai (defensive driving). A irin wannan tuki, direba kan kula da duk abubuwan da ke gefe da gefensa da kuma gaba da bayansa domin tabbatar da kare kai daga yin ragas. Ana son direba ya sanya a zuciyarsa cewa duk wadanda ke kewaye da shi ba su iya komaiba. Yin hakan zai sanya direban lura sosai don kare lafiyarsa da ta sauran mutanen, da kuma kare abubuwan hawansa da nasu daga yin ragas. A irin wannan yanayi ana son direba ya guji duk wani abu da zai iya sanya shi taka birki (brake pedal), ko taka totir (throttle pedal), kokuma juya sitiyari (steering wheel) cikin gaggawa.

  2.  TUKIN DARE



    Tukin dare wani abune mai matukar wahala musammanma ga wanda bai sababa. Anso mutum ya yi duk yadda zai iya wurin kare kansa daga yin tukin dare. Idan kuma ya zama dole mutum ya yi tukin daren to ya kamata ya tabbatar yana da cikakkiyar lafiyar ido, sannan kuma ya kasance ba mai saurin bacci bane.

    Yana da matukar mahimmanci idan direba zai yi tafiyar dare ya tabbatar da cewa gilashinsa na gaba (windscreen) da duka fitilunsa garau suke. Dole ne ya tabbatar da cewa duka fitilunsa (na gaba da na baya) suna aiki kamar yadda ya kamata. Yana da matukar mahimmanci ka kunna fitilun motarka koda kai baza su amfanekaba. Yin hakan zai taimakwa wadanda ke gabanka da bayanka su san cewa akwai mota.

    Yana da matukar mahimmancin kake rage hasken fitilarka idan kana kusa da direban da ke gabanka, ko bayanka, ko kuma idan direban da ke gaban naka ya rage hasken tasa fitilar.

    Idan za ka ajiye motarka a gefen titi, yana da matukar mahimmanci ka kunna fitilar ajiye mota (parkin lights) don nunawa mutane kasancewar motarka a wurin. Ba dolene ka kunna ita fitilarba idan wurin da haske sosai.

    Yana da kyau mutumin da ke tafiya da daddare yake yin gudu dai dai misali domin ya iya tsayawa kafin ya shiga wurin da baya iya gani.

    Idan kana cikin tafiya, direban da ke gabanka ya dalle maka ido, ya kamata ka dan rage gudu don ganinka ya dawo sosai kafin ka dora.

    Idan kana tafiya ka ji bacci na neman kamaka, baiwa wani motar ya ja. Idan kuma kai kadaine ka iya mota to, ya zama dole ka dan tsaya domin yin abin da zai kawar da yin baccin. Banda shan kwaya!

  3. TUKI A WURI ME SANTSI

    Ruwa ko mai kan sanya titi ya yi santsi ga tayoyin mota. Irin wannan yanayi na da bukatar dabarun tuki na musamman.

    Idan ana ruwa titin mota ya kanyi santsi sannan kuma yakan bawa direba wahala wurin ganin gabansa. Santsi, kan sanya mota ta dan kara tafiya akan yadda ya kamata ta tsaya idan an taka birki. A dalilin haka yana da kyau idan direba ya tsinci kansa a yanayin santsin titi ya ke kiyayewa matuka wurin bin motar da ke gabansa. Idan titi yana da santsi, ana son mutum ya kiyayi taka birki da karfi kuma dandanan; ana son mutum yake taka birkinne ahankali.

    Yan da matukar mahimmanci, idan an ruwa mai yawa, ka kunna fitulu, gaba da baya, domin nunawa wadanda ke gabanka da bayanka cewa akwai mota. Kunna fitilun gaba kuma zai kara taimaka maka wurin ganin gabanka. Yana da  kyau kayi amfani da fitila mai saukin haske (dip light).

    Anason mutum yake anfani da abar share gilashi (windscreen wiper) don share ruwa daga kan gilashin gaban motarsa. Akan sami raba a gilasan mota daga ciki, idan ana ruwan sama. Yana da matukar mahimmanci a share wannan raba tayin anfani da abar dimama mota (heater) ko kuma ta sharewa da tsumma. Yana da kyau ya kasance ba direbane zai share rabarba. Idan kuma shikadaine a cikin motar, to yana da mahimmanci ya tsaya ya share rabar kafin ya cigaba da tafiya.

    Da fatan wannan dan bayani zai anfanar.

    Ka taimaka wurun share dinshi.

    Zamu so kuma kayi like dinshi.

    Sai mun hadu a batu na gaba.

No comments:

Post a Comment