Tuesday, February 11, 2014

MANUNAN MATSALOLI A MOTA (MALFUNCTION INDICATOR LAMPS)Manunan matsaloli a mota wasu ‘yan kananan fitilu ne da ke  a ‘dashboard’ din mota da kamawarsu ke nuna cewa akwai damuwa tattare da wani abu a motar.
Za mu yi bayani dalla dalla game da wasu daga cikin irin wadannan manunan.

1.     MANUNIN MATSALAR BATIRI (BATTERY WARNING LIGHT)
Wannan fitilar na da alama kamar yadda aka nuna a kasa.


Kamawar wannan fitila na nuna cewa akwai matsala tattare da batirin mota ko janareton (alternator) mota ko kuma wasu abubuwa da ke hada batirin da janareton kamar wayoyi da dai sauransu. Dattin kafafuwan batiri da kuma tsinkewar bel (belt) da ke juya janareto na jawo kamawar wannan fitila.
Kamawar fitilar na nuna cewa batiri baya samun caji, wadda hakan zai sanya mota ta tsaya cikin gajeren lokaci.

2.     MANUNIN MATSALAR GUDANAR BAKINMAI (OIL PRESSURE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasaKamawar wannan fitila na nuna cewa bakinmai (engine oil) baya gudana a injin mota kamar yadda ya kamata, ko kuma ma baya gudana gabadaya. Abin yi ga direba a lokacin da ya ga wannan fitila ta kama shine ya tsai da motar domin duba abin da ya jawo kamawar fitilar. Rashin daukar mataki na iya jawo babbar matsala ga injin mota.
Abubuwan da ka iya jawo wannan fitila ta kama sune; karancin mai a cikin inji da matsalar fanfon bakinmai da zafin inji fiye da kima da matsalar biyarin a cikin inji da kuma toshewar hanyoyin gudanar bakinmai

3.     MANUNIN ZAFIN INJI (ENGINE TEMPERATURE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa

         


Kamawar wannan fitila na nuni da cewa injin mota ya yi zafi fiye da kima.
Kasada ce mai girma direba ya cigaba da tafiya bayan ganin wannan fitila ta kama. Dalili kuwa shine, injin mota ka iya bugawa.
Abubuwa da ke iya jawo kamawar wannan fitila sune; rashin ruwa a cikin lagireton mota da matsalar fanfon ruwa (water pump) da tsinkewar hanbel (fan belt) da matsalar fankar lagireto (radiator fan) da dattin lagireto da matsalar ‘thermostat’ (wani abu da ke hana ruwan lagireto zagayawa a lokacin tashin mota, har sai inji ya yi zafin da ya isa mota ta tashi) da kuma toshewar mafitar hayakin mota (exhaust).
Akwai hanyar sanyaya injin da ke yin zafi saboda yanayin zafin gari. Wannan hanya itace ta kunnawa, sannan kuma a kure abin zafafa mota (heater) izuwa wani lokaci.

4.     MANUNIN MATSALAR BIRKI (BRAKE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa
Kamawar wannan fitila na nuna cewa akwai matsala tattare da birkin mota. Babbar kasada ce direba ya ke tuka motarsa alhali kuma wannan fitila ta kama. Yin hakan ka iya jawo hatsari mai muni.
Abubuwan da ke jawo kamawar wannan fitila sune; karancin ruwan birki a layin birkin da matsalar abin da ke tunkuda ruwan birkin da matsalar tuwon birkin (brake pads) da kuma matsalar birkin hannu (rashin saukarsa yadda ya kamata).

5.     MANUNIN MATSALAR BIRKIN ‘ABS’
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa
‘ABS’ wata fasahar birki ce da ke kara inganci a birkin mota. ‘ABS’ kan taimaka sosai wajen rage hatsari da taka birki cikin gaggawa kan jawo.
Kamawar wannan fitila kan nuna cewa akwai matsala a fasahar ‘ABS’ din da ke kan motar.
Direba zai iya aiki da motarsa ko da kuwa wannan fitila na kunne amma kuma ya san da sanin cewa ba shi da kariyar da za a iya samu daga fasahar.
Za a iya gano matsalar ‘ABS’ ta hanyar yiwa motar gwajin na’ura maikwakwalwa. Ana amfani ne da wata na’ura da ake kira ‘scan tool’.  Ta wannan hanya kuma za a iya kashe fitilar bayan an gyara matsalar.

6.     MANUNIN KARANCIN ISKA A TAYA (LOW TIRE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasaWannan fitila na kamawa ne idan iska a daya ko sama da daya daga cikin tayoyin mota suka gaza wata ka’idar yawa.
Tafiya da tayoyi marasa isassun iska na da illa. Yin hakan ka iya jawo saurin sudewar taya da rashin dadin tafiya da karuwar shan mai da ma wasu matsalolin.

7.     MANUNIN BAIWA INJI KULAWA (CHECK ENGINE LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa
Wannan fitila na nuna cewa akwai wata matsala tattare da injin mota ko giyabos (gearbox) ko kuma ma wani abu daban da na’ura mai kwakwalwar motar (Electronic Control Module, ECM ) ta gano sannan kuma ta ajiye a kwakwalwarta.
Za a iya gano matsalar ne ta hanyar jona wata na’ura da ake kira ‘scan tool’ wadda za ta karanto matsalar da ECM din ta ajiye sannan kuma ta nuna a fuskarta (fuskar scan tool din) domin karantawa.
Bayan an gano kuma an gyara matsalar da aka gano, sai a kashe fitilar ta yin amfani da ‘scan tool’ din wadda zai goge matsalar daga kwakwalwar ECM din motar.

8.     MANUNIN BAIWA MOTA KULAWA (MAINTENANCE REQUIRED WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasaWannan fitila na nuna cewa akwai bukatar canzawa mota bakin mai (engine oil).
Idan direba ya ga wannan alama ya kamata, ko ma ya zama dole ya je a canza masa man motarsa sannan kuma ya nemi shawarar mai gyaran ko ya dace ya canza filtar bakin mai (oil filter) da filtar fetur (fuel filter) da kuma fulogai (spark plugs).
Bai kamata a ce direba ya ke jira har sai wannan fitila ta kama ba kafin ya je ya yi canjin bakinman  (wato service).

9.     MANUNIN TAKAWAR TAYOYI DAI DAI (TRACTION WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa

 
                                                   

Wannan fitila ana samunta ne kawai a motar da aka sanyawa wata fasaha da ake kira ‘Traction Control System’ (TCS).
Wannan fasaha na taimakawa wajen nunawa direba kasancewar kyakkyawan garawa ko murzawar taya akan titi.
Wannan fitila na yin fari (flashing) ne idan tana aiki dai dai. A duk lokacin da tayoyin mota suka kasance basa murzawa dai dai to wannan fitila za ta fara fari (flashing) a inda a ke son direba ya rage gudu domin samun cikakkyiyar murzawar tayoyin akan titi.
Kasancewar wannan fitila a kunne ba tare da yin fari ba na nuna cewa akwai matsala.
Hanyar da za a iya gano wannan matsalar shine ta yin amfani da ‘scan tool’ kamar yadda aka yi bayani a sama.

10.MANUNIN DAIDAITON MOTA (VEHICLE STABILITY WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa


                                  


Wannan fitila ana samunta ne kawai akan motar da aka sanyawa wata fasaha da ake kira ‘Vehicle Stability Control’ (VSC). Wannan fitila na yin fari (flashing) ne idan tana aiki dai dai.
Kasancewar wannan fitila a kunne ba tare da yin fari ba na nuna cewa akwai matsala.
Hanyar da za a iya gano wannan matsalar shine ta yin amfani da ‘scan tool’ kamar yadda aka yi bayani a sama.
Wannan shine dan takaitaccen bayanin da za mu yi.
                                                                                                                                                                                                                                                                                                                            

Wednesday, February 5, 2014

ABUBUWAN DA YA KAMATA KA SANI GAME DA TAYOYI


 
Tayoyin mota na da matukar mahimmanci wurin tafiyar da mota. Tayoyin ne ke dauke da motar da kuma dukka  abubuwan da ke cikinta.
Juyawar tayoyin kamar yadda ya kamata ne ke tafi da motar cikin nasara. Sannan kuma tayoyin ne ke taimakawa wurin tsayar da motar idan an taka birki.
Tayoyin ne kuma su ke taimakawa wurin juya motar zuwa kusurwar da ake so cikin sauki.
ABUBUWAN DA KE JAWO SAURIN LALACEWAR TAYOYI
Idan dai har mutum yana amfani da motarsa to dole ne tayoyin motar su lalace wataran. Kai, tayar mota na lalacewa ko da kuwa a ajiye kawai take! Masana sun kiyasta shekaru biyar zuwa shida a matsayin mafi tsawon lokacin da taya kan iya dauka (daga lokacin da aka yi ta). Idan taya ta wuce wannan lokacin to ta shiga yanayi na hatsari wajan amfani da ita, ko da kuwa  ma a ajiye ne ta kai tsawon wannan lokacin.
Mai yiwuwa ne ka sanya taya a yau kuma ta fashe a yau din. Abubuwa da dama ka iya jawo faruwar hakan.
Wasu daga cikin bubuwan da ke jawo lalacewar tayar mota su ne kamar haka:
1.       Bugawa tayar iska fiye da kima. Wannan ka iya jawo sudewar taya ta tsakiyarta da kuma yiwuwar saurin fashewa idan aka fada rami mai kaifi.

2.       Bugawa taya iska kasa da yadda ya kamata. Wannan ka iya kawo tsagewar taya ta gefe da gefe da kuma sudewar tayar ta gefe da gefe. Sannan kuma hakan ka iya jawo fashewar tayar.


3.       Dorawa mota kaya ko mutane fiye da kima. Abu ne mai wahala ka zubawa mota kaya, komai yawansu taya ta fashe kafin a fara tafiya. Amma muna ganin yanayi da za ka ga an dorawa mota kaya da mu kanmu za mu ga cewa ya wuce kima, idan an tafi da motar mu ga ko kuma mu ji cewa taya ta yi bindiga. Ni kaina nan ganau ne akan faruwar hakan! Allah ne ya yi da sauran shekaruna. Alhamdulillah! Babban hatsari ne a zubawa mota kaya fiye da kima. Yawan nauyin kaya shine yawan wahalar da tayar mota kan fuskanta wanda hakan kuma zai jawo saurin lalacewar tayoyin motar.

4.       Gudu fiye da kima. Kowacce taya na da iya gudun da za a iya yi da ita. Tafiya da mota a gudun da ya wuce wadda aka kayyade ma taya (kamar yadda aka rubuta a jikin tayar) ka iya jawo fashewarta. Sannan ma ko da mutum bai kai iyakar ba, yawan gudu da mota shine yawan wahalar da tayoyinta wadda kuma hakan zai janyo saurin lalacewar tayoyin.


5.       Yawan taka birki. Dole ne mai tuka mota ya taka birki. Idan mutum baya son ya taka birki to kada ya tuka mota. Wannan kuma ba yana nufin muke taka birki ba gaira ba dalili ba, sannan kuma ba yana nufin mu ke cin taya ba! Cin taya da kuma taka birki na ba gaira ba dalili kan jawo saurin sudewa ko kuma lalacewar tayoyi.

6.      Dagawar gaggawa da tsayawar gaggawa


7.       Ajiye mota a wurin da bai dace ba. Ajiye mota a wurin da ke da duwatsu ko duk wani abu da ka iya loma taya na da matsala akan taya.

8.       Sanya taya ba dai dai ba. Sanya taya ba dai dai ba ka iya jawo fashewarta a lokacin da ake tafiya da mota. Sannan rashin kula wurin sanya tayar ma ka iya jawowa mai sanya tayar ya yi mata lahanin da ka iya jawo illa.


9.       Yanayin titi. Titi mai yawan tsakuwa ko kuma mai yawan ramuka (idan direba na fadawa ramukan) kan iya taimakawa wurin sanya taya ta mutu da gaggawa.

10.   Yanayin zafi ko sanyi. Abin da kusan kowa ya sani ne cewa tayar mota tafi samun matsala a lokacin zafi. Yau da gobe ya sanya an gano cewa tayar da akan sanya alokacin sanyi kan fi wacce aka sanya a lokacin zafi dadewa. Dalilin haka kuwa shine, dan sudewar da tayar za ta yi kafin lokacin zafin zai taimaka ta zamo mai saurin sanyaya daga zafin gurzar titi a lokacin tafiya a lokacin yanayin zafi.


YA ZA MU GANE TAYARMU?Misalan Bayanan Taya


Tayar mota na dauke da wasu mahimman bayanai da ya kamata duk wani mai amfani da mota ya sani. Kash! Amma kashi fiye da casa’in na masu amfani da motar ba su kula da wannan bayanan.
Akan rubuta wadannan bayanai ne a gefen tayar daga waje (gefen da za ka iya gani bayan an daura tayar a jikin rim).
Za mu dauke su daya bayan daya mu yi bayani akansu:
1.       Na farko da za mu yi bayani akai shine yawan iskar da ya kamata a bugawa taya. Wannan bayani na zuwa ne da wasu lambobi sannan kuma da haruffa guda uku kamar haka: 24psi (150Kpa). Wannan na nuna iya yawan iskar da za a iya bugawa tayar. Buga iska ya wuce wannan awun ka iya jawo matsala ga taya.

2.       Na biyu kuma shine rubutun da za ka ga an yi lambobi biyu da kuma harafi daya a bayansu. Misali; 86H. lambobin guda biyun na nuna iya nauyin kayan da tayar za ta iya dauka ne, a inda kuma harafin ke nuna iya gudun da tayar za ta iya jurewa.
Misalan ma’anar lambobin da ke nuna nauyin sune kamar haka:                                                                                                    

71=345Kg
75=387Kg
79= 437Kg
80=450Kg
85=515Kg
90=600Kg
95=690Kg
100=800Kg
105=925Kg
110=1060Kg
Kasada ce babba dorawa mota abubuwa masu nauyi fiye da wadda aka kayyadewa tayoyin kamar yadda aka rubuta a jikinsu.
Misalan ma’anar haruffan da ke nuna tafiya (gudu) sune kamar haka:

L= 120Km/h
M= 130Km/h
N= 140Km/h
P= 150Km/h
Q= 160Km/h
R= 170Km/h
S= 180Km/h
T= 190Km/h
U= 200Km/h
H= 210Km/h
           V=240Km/h
              Z= Sama da 240Km/h
 W= 270Km/h
                  (W)= Sama da 270Km/h
Y= 300Km/h
                 (Y)= Sama da 300Km/h
Kasada ce babba yin gudu a mota fiye da wadda aka kayyade ma tayoyin motar kamar yadda aka rubuta a jikin tayoyin. Idan ka san kana da gudu sai ka nemi tayoyi dai dai da kai! Ina ‘yan Vectra din Jos zuwa Bauchi, ko Jos zuwa kano da kuma ‘yan Golf din Kano zuwa Abuja? Wacce ya kamata ku daura? Ha ha ha......

3.       Na uku kuma shine rubutu da za ka ga anyi kamar haka: P205/75R14. Harafin farko, wato ‘P’ na nufin irin motar da ya kamata a daura ma tayar. ‘P’ na nufin motar daukar  fasinja wato, tayar ta motar fasinja ce.  Abu na gaba kuma wato, 205/75 na nuna yanayin girman tayar. ‘205’ na nufin fadin tayar (ta wurin da ta ke taka titi), a ma’aunin millimetre. ‘75’ na nufin abin da za a samu idan aka raba tsayin tayar (daga inda ta ke taka titi izuwa inda ta ke taba rim) da kuma fadinta (kamar yadda mu ka fada), sannan kuma aka yi sau da dari wato: Tsayi/Fadi X 100. Lambobi biyu kuma na gaba wato, ‘14’ na nuna girman wili (rim) din tayar a ma’aunin inci (inches).

Fadi da tsayin Taya


4.       Na hudu kuma shine rubutu da za ka ga an yi kamar haka: 3607 (foto na kasa). Wannan ya na nuna lokacin da aka yi tayar daga kamfani. Lambobi biyun farko ‘36’ na nuna satukan shekara, a inda kuma lambobi biyun karshe ‘07’ ke nuna shekarar. Lambobin ‘3607’ na nuna cewa an yi tayar ne a sati na talatin da shida (36) na shekarar dubu biyu da bakwai (2007).

Lokacin da aka yi taya


Sanin lokacin da aka yi taya na da matukar mahimmanci wajan gane lokacin da tayar za ta gama aikinta. A ka’ida, idan taya ta yi shekaru biyar zuwa shida aikinta ya kare, ko da kuwa a ajiye ta ke.
Misali, hatsari ne babba, a wannan shekara ta 2014 da mu ke ciki mutum ya shiga motar da ke da  tayoyin da aka rubuta 0206 a jikinsu, ko da kuwa tayoyin sun yi kama da sababbi ne.
Ina ga dai haka za mu tsaya game da bayani akan tayoyi.
Lokaci ya yi da za ka je jikin motarka don yin bincike akan tayoyinka.
Allah ya tsaremu.