Thursday, July 5, 2012

MOTOCI: Ya Su Ke?

Mun kirkiro wannan shafin yanar gizo ne na Zauren Motoci domin mu ke bawa mutane shawarwari game da yadda za su ke tafi da abubuwan hawansu domin samun cikakkiyar morewa abubuwan hawan nasu.

Kafin mu fara ba da shawarwari akan yadda za ake tafi da abubuwan hawan, ya kamata mu dan yi bayani game da su abubuwan hawan da kuma yadda suke aiki.

 

Mota ko kuma 'motor vehicle', a turance, abar hawace da ke da tayoyi guda hudu kuma ta ke iya tafiyar da kanta ta hanyar sarrafata da mahayinta kan yi.

Kowacce mota na da abubuwa ko bangarori guda shida (6) kamar haka

  1. Gangar Jiki ko kuma 'Body' a turance

  2. Madaukai ko kuma 'Suspension' a turance

  3. Gidan Wuta ko kuma 'Engine' a turance

  4. Majanyai ko kuma 'Transmission' a turance

  5. Masarrafa ko kuma 'Controls' a turance

  6. 'Yan Agaji ko kuma 'Auxiliaries' a turance

Yanzu za mu daukesu daya bayan daya mu dan yi bayani akansu

 

GANGAR JIKI (BODY) 

Gangar jikin mota wani sashi ko kuma bangarene na motar da ke kunshe da yawancin abubuwan da suka hadu su ka hada motar. Sauran abubuwan kuma da ba a cikinsa su ke ba suna makale ne a jikinsa.

A cikin gangar jikin mota ne kujeru da ake zama suke, a jikin gangar jikin motarne kuma ake sanya injin motar, a kuma jikin gangar jikin motarne ake makala fitulun motar da dai sauransu.

MADAUKAI (SUSPENSION)

Madaukan mota sune su ke dauke da gangar jikinta da kuma duk abubuwan da ke cikinsa da kuma wadanda su ke makale a jikinsa.

Madaukan mota sun hada da sifirin (spring) da tayoyi (tires) da shakzoba (shock absorber) da kuma sandunan karfen da tayoyi ke juya a jikinsu wato azil shaf (axle shafts).

 

GIDAN WUTA KO INJI (ENGINE)

Gidan wuta ko inji shine ke bawa mota karfin da ta ke bukata domin ta yi tafiya. Inji ya kunshi abubuwa da yawa wadanda ke aiki tare domin su bayar da karfin da zai iya tafi da mota.

MAJANYAI (TRANSMISSION)

Majanyan mota sune ke yin amfani da karfin juyawa da inji ya samar domin su mikawa tayoyi don su juya su tafi da mota.

Majanyai sun hada da abin da ake kira kuloci (clutch) da giyabos (gearbox) da farfela (propeller shaft) da kuma kundu (differential).

 

'YAN AGAJI (AUXILIARIES)

'yan agaji sune abubuwan da ke tallafawa mota ta aiwatar da aikinta na tafiyar da mutum da kayansa kamar yadda ya kamata.

'Yan agaji sun hada da batiri (battery) da janareta (generator) da kistata (starter motor) da fulogi (plugs) da bobin (ignition coil) da ham (blow horn) da radio (radio receiver) da iyakwandishin (air condition) da dai sauransu.

Mota za ta iya tafiy kamar yadda ya kamata ba tare da da yawa daga cikin 'yan agaji ba.

1 comment:

  1. Allah ya saka maku da alkhairi wannan shafi ya yi. Allah ya kara kwakwalwa.

    ReplyDelete