Thursday, November 15, 2012

RASHIN TASHIN MOTA: ME KE KAWO SHI? 1


Akwai damuwa ace ka shirya tsaf domin fita, ka zo ka  shiga motarka ka tasheta amma ta ki tashi. Haka nan, akwai damuwa ka ajiye motarka don zuwa ka yi wani uzuri ka dawo, bayan ka dawo ka tashi motar taka ta ki tashi. Tabbas akwai damuwa kana cikin tafiya motarka ta mutu, kayi, kayi, taki tashi.
Shin me ke kawo rashin tashin mota?
Yau shine abin da za mu mai da hankali akai.
Akwai abubuwa da dama da zasu iya sanyawa mota taki tashi. Za mu iya kasa wadannan abubuwa izuwa gida biyu kamar haka:

  1. Ya kasance ka sanya makullinka a cikin makunnar mota, ka juya ka ji shiru, sai dai kyat...kyat.. kawai.
  2. Ka juya makullin tashin mota ka ji kistata (starter motor) na juyawa amma mota ta ki tashi.
                        
Yanzu za mu daukesu daya bayan daya mu yi bayani.


  1. YA KASANCE KA SANYA MAKULLINKA A CIKIN MAKUNNAR MOTA, KA JUYA KA JI SHIRU
Abubuwan da ka iya jawo wannan matsalar sune kamar haka:
  • MATSALAR FIS FIS (FUSES)
Idan ya kasance fis da ya shafi bangaren tashin mota ya lalace ko kuma ya goce.

Fis (fuse) na mota

  • MATSALAR BATIRI (BATTERY)
Idan ya kasance babu caji a batiri ko kuma ya kasance kafafun batirin (battery terminals) sun yi datti. Idan matsalar batirin ba ta yi kamariba, kistata za ta iya juya inji amma ba zai tashiba.
  • MATSALAR MAKUNNA (IGNITION SWITCH)
Idan makunnar mota (abin da ake zira makullin tashin maota a cikinsa) na da matsala, mota za ta iya kin tashi. Za ka iya tunanin cewa makunnarka na da matsala ne idan ka tabbatar cewa batirinka da fis fis dinka kalau suke, sannan kuma, ka ga dukkanin jajayen wutar dash (dash board) dinka ba su kama ba. Haka kuma ka kunna fitila (headlights) ka ga haskensu bai ragu ba a take, lokacin da ka juya makullin tashin motar.
  • MATSALAR RILE (RELAY) NA KISTATA (STARTER MOTOR)
Idan rile din kistata ya lalace ko kuma ya goce, kistata ba za ta sami wutar lantarki daga batiri ba, ballantana har ta juya injin mota, motar ta tashi.

Rile (Relay)

  • MATSALAR SALANOY (SOLENOID)
Salanoy wani abune da ke a jikin kistata. shi dai kamar wata makunna ce ta musamman ga kistata. Idan salanoy ya sami matsala kistata ba za ta yi aiki ba.
Kistata (starter motor). Wannan kundiguilin na sama shine salanoy (solenoid)


  • MATSALAR KISTATA
Idan kistata ta mutu gaba daya, baza ta juya ba ballantana ta juya injin mota, motar ta tashi. Idan kuma kistata tana juyawa amma ta kasa tashin mota sannan kuma kana jin wata kara da ta wuce misali, to akwai matsala a jikin kistatar ko hakoranata ko kuma hakoran firawil (flywheel).
Idan kistata na juyawa ahankali ko kuma da kyar, to wannan ka iya kasancewa matsalar batiri ce.
  • MATSALAR KARIYAR TSAUTSAYI (SAFETY SWITCHES)
Ana sanyawa motoci wasu makunnai na musamman domin kawar da matsalar tafiyar mota a dai dai lokacin da ake ta da ita.
Mota mai kuloci wato, 'manual' ana sanya mata abin da ake kira a turance 'clutch safety switch'. Idan mota na da irin wannan makunna ba za ta tashi ba har sai direba ya take kuloci a lokacin tayar da ita.
Haka kuma mota marar kuloci wato, 'auto' ana sanya mata abin da ake kira a turance 'park or neutral' safety switch' ko kuma 'Brake pedal safety switch'. Irin wannan motar za ta tashi ne kawai idan  har sandan zabar giyar motar baya kan 'neutral or N' ko kuma baya kan 'park or P' ko kuma idan direba ya take birki a lokacin tayar da ita.
Idan irin wadannan makunnan na musamman sun sami matsala, mota ba za ta tashi ba gaba daya.
Amma wasu sukan je a cire masu irin wadannan makunnan tsaro daga motocinsu idan sun kasance suna basu matsala. Amma fa suna da anfani sosai. Sai dai in har za ka iya kiyayewa!
  • MAKALEWAR INJI (ENGINE SEIZURE)
Injin mota zai iya makalewa yadda kistata ba za ta iya juya shi ba gabadaya.
Wannan kan faru ne idan aka sami matsalar biyari (bearing) ko kuma shigar ruwa cikin tukwanen gashi (engine cylinder) saboda lalacewar 'gasket'.
  • MATSALAR SAKYURITI (SECURITY)
Wasu sukan sanya sakyuriti yadda zai hana juyawar kistata gabadaya idan an zo ta da mota ba da sanin mai ita ba.
Idan aka sami matsala a irin wannan sakyuriti kistata ba za ta motsaba a lokacin da aka zo ta da motar.
  • MATSALAR WAYA (WIRING)
Rashin tashin mota kan faru idan akwai matsala a wata daga cikin wayoyin da ke da alhakin dauko wutar lantarki  daga batiri. Zai iya kasancewa wayar ta tsinke ko kuma wayoyi su hadu da juna ko kuma ma waya ta kone.
Akwai bukatar duba wayoyi a lokacin da mota ta ki tashi.
Karshen kashi na farko na wannan bayani ke nan. Sai mun hadu a kashi na biyu.
Allah ya sa wannan bayani ya amfanar.
Kada a manta, idan akwai tambaya sai a rubuta a 'comment box' da ke kasa. 
Ka iya Like mu. Za mu ji dadin hakan.



No comments:

Post a Comment