Monday, July 23, 2012

ABUBUWAN KULAWA GA MAI SAYEN MOTA


Akwai abubuwan kulawa sosai idan mutum ya tashi sayen mota. Ganin cewa hausawa na cewa zuwa da kai yafi sako, shi yasa muka ga ya dace mu sanar da ku abubuwan daya  kamata ku yi, ku da kanku, alokacinda zaku sayi motar da ba sabuwaba, domin rage cutarwa da akan yiwa masu sayen motocin da ba sababbiba.

Asha karatu lafiya.

Kafin komai, yana da kyau motar da kake son saya din ta zamana injinta bai da zafi alokacin da zaka dubata, sannan kuma  a ajiyeta a wuri mikakke wanda bai jirkitaba. Sannan ka tabbatar akwai isasshen haske a wurin da zaka duba motar da zaka saya din.

1.       DUBA WAJEN MOTA

Ka zagaya motar ka tabbatar ba wani bangare daya jirkita. Jirkitawar wani bangare na nuna matsalar sifirin ko kuma matsalar madaukai.

 

Ka danna kusurwoyin motar ka gani. Idan motar ta rika yin sama da kasa fiye da sau daya kokuma, a wasu lokutan fiye da sau biyu to tana da matsalar shakzoba (shockabsorber).

 

Ka sanya hanunka a sama da kasan tayoyi motar,  ka rkikesu ka ke jijjigasu daya bayan daya. Idan ka ji taya na motsi ko kara to akwai matsalar wilbiyari (wheel bearing) ko matsalar madaukai kokuma dukka biyun.

 

TAYOYI

Ka duba tayoyin ka tabbatar kalau suke. Idan kuma akwai sudewa to ka tabbatar sudewar tasu ta bai dayace. Idan kaga taya ta sude ta gefe daya to akwai matsalar madaukai. Ka duba yanayin sudewar tayoyin. Duk tayar da ta sude har ramin tayar ayawancinta ya yi kasa da milimita daya da rabi (1.5mm) to tana bukatar canzawa.

 

Ka duba tayoyin sosai domin ka tabbatar da cewa babu wani wuri da ta bullo ko ta yi rami ko yaya.

 

Ka kuma duba rim din tayoyin ka tabbatar da babu wani lomewa ko launewa mai kamari. Idan akwai to motar na da matsalar madaukai (suspension)

 

Ka tabbatar da cewa tayoyin motar iri dayane.

 

GANGAR JIKIN MOTA

Ka duba jikin motar gaba daya. Ka duba ka gani ko akwai tsatsa ko karjiya ko kuma lomewa a jikin motar. Duba motar sosai zai iya nuna  maka ko motar ta taba yin hatsari ko kuma an taba canza mata fantine. Sayan motar da ta taba yin hatsari kasadace a wasu lokutan, barinma idan kasanta (chasiss) ya tabu. Hakan ka iya janyo cin tayoyi.

Ka duba sosai ko an taba bugar wani bangaren motar kamarsu, gefe da gefe da kofofi da gaba da kuma baya.

Idan an taba yiwa motar fanti zai yi wuya ka kasa ganin wani wuri da fanti ya yi yawa ko kuma ya taba wurin da bai kamata ya tababa. Ta irn nan ne zaka iya gane ko an taba yiwa mota fanti.

 

GILASHI

Yana da matukar mahimmanci ka duba gilasan motar gaba daya domin ka tabbatar basu da wata tsaguwa da zata iya zamewa matsala. 

 

FITILU

Ka duba duka fitilun motar ka tabbatar ba wata tsaguwa ko fashewa a jikinsu. Kuma ka kunnasu daya bayan daya ka tabbatar duka suna aiki.

 

2.       DUBA CIKIN MOTA

WARI

Ka tabbatar da cikin motar baya wari, idan kuma yana yi, ka tabbatar da me ya kawo warin. Mota kan yi wari idan ruwa yana shiga cikinta. Kada ka sayi motar da take yayyo har sai ka san me kake saya. Yayyon mota na da wahalar gyarawa wasu lokutan.

 

KUJERU

Ka duba kujerun motar sosai ka tabbatar da cewa basu ji jikiba. Ka kuma duba sosai ka tabbatar da cewa duka abubuwan sarrafa kujerun suna aiki kamar yadda ya kamata.

Idan kaga kujeru sun ji jiki sannan kuma abin nuna tafiyar mota (odometer) bai ja sosaiba to an rageshine; sai kasan irin sayen da zaka yiwa motar. Hakanan idan kaga kujeru sababbi amma kuma abin nuna tafiyar mota ya ja sosai  to kada ka kalli kujerun kace ka sayi motar da bata dadeba. Sai ayi hattara! Ammafa a sani akwai hanyoyi da yawa da dillalan mota zasu iya caka maka. Idan kana tsoro, ka sami wanda ya san sirrin mota ku yi wannan binciken tare.

 

ROBOBI

Ka duba duka robobin da ke cikin motar musammanma na jikin matakin kuloci (clutch pedal) da na jikin matakin totir (throttle pedal) da na jikin matakin birki (brake pedal). Idan kaga wadannan robobi sun ci sosai to akwai alamun cewa motar ta jima ko kuma direban da yai amfani da ita yana yi masu takawar ba gaira ba dalili, wanda hakan na da illa ga mota, barinma ga kuloci.

 

TAYAR DA MOTA

Anso ka tayar da motar domin ka tabbatar cewa bata da matsalar tashi. Ka barta ta danyi sulo (idle) domin ka tabbatar cewa bata da matsala.

 

 

 

MANUNAI DA MATAIMAKA

Ka duba ka tabbatar kowanne manuni  kamarsu abinda ke nuna yawan mai a motar (fuel guage), ko abin da ke nuna yanayin zafin inji (temperature guage), ko abin da ke nuna gudun mota (odometer) da dai sauransu suna aiki kamar yadda ya kamata.

Sannan ka tabbatar da duka abubuwan da ke sarrafa dagawar gilasai, da wadanda ake amfani dasu wurin budewa da rufe kofa da dai sauransu suna aiki kamar yadda ya kamata.

Rashin aikin wasu daga cikin abubuwan da muka zaiyana na iya jawo gyara mai yawa. Sai ayi hattara!

Ka danna ham da abar sanyaya mota (car AC) da abar dimama motar (car heater) ka tabbatar duk suna aiki. Ka duba duka makunnan fitilu ka tabbatar duka suna aiki kamar yadda ya kamata.

Ka duba rediyo itama ka tabbatar tana aiki kamar yadda ya kamata.

 

3.       DUBA INJIN MOTA

Kada ka damu da kura a jikin inji. Babban abinda zaka duba shine kasancewar  feshin bakinmai a jikin abubuwa a wajen injin. Sannan ka duba yanayin wayoyi . Sannan  yana da kyau ka duba  yanayin kafofin batirin motar.

 

MAYUKA

Ka duba yanayin man birki (brake fluid) da man sitiyari (steering oil) da man kuloci (clutch fluid) da kuma man batiri (electrolyte). Yanayin wadannan mayuka da muka bayyana zai nuna irin direban da yai amfani da motar. Idan direban mai kulane zaka sami wadannan mayuka kamar yadda ya kamata kuma basu fantsamo wajeba.

 

WAYOYI DA TIYO-TIYON MAI DA SAURANSU

Ka duba ka tabbatar duka wayoyi kalau suke basu tsatstsageba. Wayoyi da suke a gutsitstsire na nuna direba marar kulawa da mota kuma, sayan irin wannan motar na da hatsari. 

Ka duba akwatin fis fis (fuse box) ka tabbatar da cewa duka suna nan kalau. Idan ka ga an sanya wayoyi a maimakon fis to ka sayi motar da kulawa domin direban ba mai kulawa bane.

 

Ka duba duka tiyo-tiyon mai ka tabbatar basu da tsaguwa ko wani lahani.

 

Ka duba hambel (fan belt) da duka sauran bel-bel ka tabbatar garau suke ba wani tsagewa a jikinsu.

 

LAGIRETO

Ka duda lagireton motar sosai ta ko’ina ka tabbatar garau yake. Ka duba ka tabbatar bai yi dattiba. Yin dattinsa zai iya kasancewa bindiga ciki da mugunta, abin nufi anan shine, zai iya kasancewa ya haifar da matsalar da zata iya fara nunawa akanka bayan ka sayi motar.

 

DUBA KARKASHIN MOTA

Ka duba karkashin motar ka tabbatar babu yoyon bakinmai ko kuma duk wani irin mai. Ka duba robobin dirabin shaf (C-V joints boots) ka tabbatar cewa basu tsageba.

 

Ka duba salansa (tail pipe). Ka sa hannunka a ciki ka gogo, ka tabbatar da babu laima a jikin dussar hayakin da ke makalewa a salansar. Ka tabbatar salansar bata yi tsatsaba sannan kuma babu walda a jiki, idan kuma akwai sai ka san irin cinikin da zaka yi.

 

4.       GWAJI

Bayan yin dukka abubuwan da muka zayyana a sama abin daya rage ayanzu shine hawan motar domin yin gwaji. Yana da kyau kayi tafiyar kamar  akalla minti 20 da motar domin ka tabbatar da yadda take aiki.

 

Farko ana son ka shiga motar ka sanya madauri (seat belt)  domin kaji yanayin jin dadin zamanka a motar.

Daganan sai ka tashi motar ka barta ta yi sulo. Ka tabbata tana yin sulo yadda ya kamata.

 

Sai ka juya sitiyarin motar gefe da gefe ka tabbatar bashi da matsala.

 

Sai ka fara tuka motar. Anan zaka fara jin yanayin lafiyar giyabos (gearbox) da kuloci (clutch).

Idan ka daga ya kamata motar ta tafi ba tare da wata jijjigaba.

 

Idan kana tafiya natse kuma akan titi mai kyau, bai kamata ace motar na gyulu-gyulu ko jijjigaba.

 

Daga nan sai ka sami hanya mai dan tudu da kwari, ka kai motar kimanin yanyin tafiyar kilomita hamsin a awa daya (50Km/h). Bai kamata ka ke jin kyukyu-kyukyu a wannan yanayiba in har motar kalau take. Idan kuma ka ji motar na jiijjiga sosai to akwai matsalar madaukai a motar.

 

Idan kuma ka hau hanya mai kyau ka kama gudu sosai ka ji sitiyarin motar yana rawa to motar na da matsalar alamin (wheel alignment) ko balansin (wheel balancing) ko kuma dukka. Amma kuma wataran rashin isashshiyar iska a wasu tayoyi kan sanya wannnan matsalar. Duka wadannan abubuwane masu saukin gyara.

 

Idan zaka gwada birki sai ka sami wurin da babu kowa ka kara gudun motar kamar kilomita saba’in a awa daya (70Km/h) sannan ka taka birkin. Idan ka yi hakan ya kamata motar ta tsaya ba tare da ta fizgeka, kubi da kubiba. Sannan kuma ya kamata ya zamana birkin bai yi tauri ko laushi sosaiba alokacin takawar. Ka gwada hakan kamar sau hudu ko fiye da hakan.

Ka kuma tabbata birkin baya kara alokacin da ka takashi.

A karshe kuma ka gwada birkin ajiye mota (parking brake) domin tabbatar da yana aiki.

Da fatan abin da muka bayyana maku zai yi amfani.

Allah ya taimaka mana .

Idan kana da tambaya sai ka aiko mana ta : zaurenmotoci@gmail.com , ko kuma ka rubuta tambayar taka a ‘comment box’ din da zai bayyana bayan ka latsa Kalmar ‘comment’ da ke kasa.

Sai mun hadu a batu na gaba.

 

 

 

No comments:

Post a Comment