Saturday, July 21, 2012

TUKI ALOKACIN MATSALA



A baya munyi bayani game da dabarun tuki akan titi da kuma, dabarun tuki  a wasu lokuta na musamman. Yau za mu yi bayanine game da yadda mutum ya kamata ya sarrafa motarsa, alokacin da wata matsala ta afku yayin da yake tuki.

Asha karatu lafiya.

1.       TUKI ALOKACIN ZAMEWAR TAYA

A wasu lokutan, musammanma alokacin da ake ruwan sama ko kuma, akan titin da ke da tsakuwoyi , ko kuma alokacin da direba katsam ya taka birki ko ya juya sitiyari,  tayar mota kan iya rasa kamawar da take yiwa titi saboda santsi. Wannan kan iya sanyawa taya ko tayoyi su zame wanda hakan ka iya sanya direba ya rasa damar sarrafa motar. Wannan yanayi ka iya janyo hatsari da zai iya sanya asarar rayuka. Allah ya kyauta.

Akwai abinda direba ya kamata ya yi domin kare afkuwar hatsari alokacin faruwar zamewar taya ko tayoyin mota.

Abin da kan faru idan tayoyin gabane suka zame shine; motar zata mikene sosai a maimakon take bin juyawar sitiyari. Idan zamewar tayar ya farune saboda taka birki katsam, to sai ka dan sassauta ka taka birki a natse ka kuma tsaida kan motar (wato sitiyari). Idan kuma zamewar tayar ya farune saboda gudu mai yawa (wayaga fanfalaki), sai kai maza ka cire kafarka daga kan totir sannan ka tsai da kan motar ka kuma taka birki ahankali.

 

Abin kuma da kan faru idan tayoyin bayane suka zame shine; motar zata fizgekane gefe.

Idan hakan ta faru, saika juya sitiyari a natse domin ka dawo da motar yadda ya kamata. Kada ka firgita har ka juya sitiyarin ya wuce yadda ya kamata. Juya sitiyarin fiye da yadda ya kamata ka iya jawowa motar ta yi yawo wadda hakan na da matukar hatsari. Ka tabbata ba ka taka totirba har zuwa lokacin da ka sami kan motar!

 

2.       TUKI ALOKACIN FASHEWAR TAYA

Idan taya ta fashe mota kan fizgi direbane  zuwa wani bangare. Idan hakan ta faru sai mutum ya taka birki ahankali kuma, a natse sannan ya rike sitiyari da karfi ya nemi wurin da zai tsaya a gefen titi. Taka birki da karfi na da matukar hatsari a irin wannan yanayi!  Kada mutum ya kuskura ya taka totir a irin wannan yanayi!

 

3.       TUKI ALOKACIN KWALEWAR BIRKI

Hausawa kan ce “karfen nasara baka da tabbas”. Wannan haka yake. Akwai wasu lokuta da birki kan yiwa direba bazata. Idan irin wannan bazata ta faru wato, katsam birki ya kwale kana cikin zura gudu, yaya zakayi?

Idan birkinka yakwale ana so kake taka birkin kana dagawa da sauri da sauri abin da ake kira a turance ‘pumping’, sannan ka canja giyar motar zuwa babbar giya, sai kuma ka ja birkin ajiye mota (parking brake). Idan kana tsoron tsayawa akan titi saboda ragas sai ka bar kan titin. Ka tuna idan yin ragas ya zama dole, sai ka durfafi wurin da kasan zai fi maka sauki idan aka hadu!

Allah ya kyauta.

Tuki acikin ruwa kan rage karfin birki. An so da ka fita daga cikin ruwan ka ke tafiya ahankali sannan kuma ka dora kafarka akan birki ahankali zuwa dan wani lokaci, don birkin ya bushe.

 

4.       TUKI ALOKACIN RAGAS

Allah ya kyauta. Wataran akan sami yanayi da kansa mota da mota su hadu da juna,  wato ayi ragas. Akwai wasu direbobin da duk yadda ka yi das u sai sun janyo maka jangwam. Irin wadannan direbobin kan kasance kodai ‘yankwayane, kokuma  wadanda hanunsu bai fadaba kuma suke jin sun wuce makala ‘L’ a motarsu. Da zasu makala ‘L’ din da sai ka gane cewa sabon hanune kasan yadda za ka bi dasu.

Wasu direbobin da kan jawo ragas kuma baccine yake daukarsu sannan kuma saboda wasu dalilai da, su suka sanma kansu, ba za su tsaya su yi abin da zai tafi da baccin nasu ba kafin su dora akan tafiyar tasu.

Wasu kuma kan jawo ragas ne saboda rashin kula da gyaran motarsu, wasu kuma saboda rashin bin dokokin hanya dana tuki.

Ragas kan farune ta gaba da gaba ko ta gaba da baya ko ta baya da baya (wadda keda wahalar afkuwa).

Idan ragas zai faru ta gaba da gaba, kada ka firgita, kada kuma kai saurin juya sitiyari domin baka saniba ko daya direbanma nan yake son ya juya. A maimakon haka sai ka kunna fitila ka kuma danna ham domin fargar da direban. Bayan haka sai ka duba hagun dinka domin ganin yiwuwar komawa  bangaren. Idan akwai bukatar tsayawa sai ka sauka daga kan titi ka tsaya.

 

Zai iya yiwuwa ayi ragas ta gaba da baya, inda wani zai buga wa mota ta baya (wato abin da wasu ke kira; Karin gudu). A irin wannan yanayi an so wanda aka bugawa din ya natsu ya kalli gefe da gefensa don ganin ko akwai mota. Kada yai saurin taka birki. Zai rike kan sitiyarinsa gam yadda zai kare kansa daga yawo sannan kada ya soma ya taka totir. Daga nan sai ya nemi wurin da zai tsaya a kasan titi domin jiran abin da zai biyo baya.

Ya zama dole ga duk wanda ya ajiye mota a gefen titi don faruwar wata matsala ya sanya alama akan titin domin nunawa mai zuwa cewa akwai mota a wurin. Rashin yin haka kan haddasa hatsari a lokuta da dama! Ni kaina ya taba jawo mani.

Allah yasa dan abin da muka fada ya anfanar.

Sai mun hadu a batu na gaba.

Mai tambaya zai iya aiko mana ta akwatun yanar gizonmu: zaurenmotoci@gmail.com ko kuma ya rubuta a ‘comment box’ din wannan makala a kasa.

No comments:

Post a Comment