Tuesday, February 11, 2014

MANUNAN MATSALOLI A MOTA (MALFUNCTION INDICATOR LAMPS)



Manunan matsaloli a mota wasu ‘yan kananan fitilu ne da ke  a ‘dashboard’ din mota da kamawarsu ke nuna cewa akwai damuwa tattare da wani abu a motar.
Za mu yi bayani dalla dalla game da wasu daga cikin irin wadannan manunan.

1.     MANUNIN MATSALAR BATIRI (BATTERY WARNING LIGHT)
Wannan fitilar na da alama kamar yadda aka nuna a kasa.


Kamawar wannan fitila na nuna cewa akwai matsala tattare da batirin mota ko janareton (alternator) mota ko kuma wasu abubuwa da ke hada batirin da janareton kamar wayoyi da dai sauransu. Dattin kafafuwan batiri da kuma tsinkewar bel (belt) da ke juya janareto na jawo kamawar wannan fitila.
Kamawar fitilar na nuna cewa batiri baya samun caji, wadda hakan zai sanya mota ta tsaya cikin gajeren lokaci.

2.     MANUNIN MATSALAR GUDANAR BAKINMAI (OIL PRESSURE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa



Kamawar wannan fitila na nuna cewa bakinmai (engine oil) baya gudana a injin mota kamar yadda ya kamata, ko kuma ma baya gudana gabadaya. Abin yi ga direba a lokacin da ya ga wannan fitila ta kama shine ya tsai da motar domin duba abin da ya jawo kamawar fitilar. Rashin daukar mataki na iya jawo babbar matsala ga injin mota.
Abubuwan da ka iya jawo wannan fitila ta kama sune; karancin mai a cikin inji da matsalar fanfon bakinmai da zafin inji fiye da kima da matsalar biyarin a cikin inji da kuma toshewar hanyoyin gudanar bakinmai

3.     MANUNIN ZAFIN INJI (ENGINE TEMPERATURE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa

         


Kamawar wannan fitila na nuni da cewa injin mota ya yi zafi fiye da kima.
Kasada ce mai girma direba ya cigaba da tafiya bayan ganin wannan fitila ta kama. Dalili kuwa shine, injin mota ka iya bugawa.
Abubuwa da ke iya jawo kamawar wannan fitila sune; rashin ruwa a cikin lagireton mota da matsalar fanfon ruwa (water pump) da tsinkewar hanbel (fan belt) da matsalar fankar lagireto (radiator fan) da dattin lagireto da matsalar ‘thermostat’ (wani abu da ke hana ruwan lagireto zagayawa a lokacin tashin mota, har sai inji ya yi zafin da ya isa mota ta tashi) da kuma toshewar mafitar hayakin mota (exhaust).
Akwai hanyar sanyaya injin da ke yin zafi saboda yanayin zafin gari. Wannan hanya itace ta kunnawa, sannan kuma a kure abin zafafa mota (heater) izuwa wani lokaci.

4.     MANUNIN MATSALAR BIRKI (BRAKE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa




Kamawar wannan fitila na nuna cewa akwai matsala tattare da birkin mota. Babbar kasada ce direba ya ke tuka motarsa alhali kuma wannan fitila ta kama. Yin hakan ka iya jawo hatsari mai muni.
Abubuwan da ke jawo kamawar wannan fitila sune; karancin ruwan birki a layin birkin da matsalar abin da ke tunkuda ruwan birkin da matsalar tuwon birkin (brake pads) da kuma matsalar birkin hannu (rashin saukarsa yadda ya kamata).

5.     MANUNIN MATSALAR BIRKIN ‘ABS’
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa




‘ABS’ wata fasahar birki ce da ke kara inganci a birkin mota. ‘ABS’ kan taimaka sosai wajen rage hatsari da taka birki cikin gaggawa kan jawo.
Kamawar wannan fitila kan nuna cewa akwai matsala a fasahar ‘ABS’ din da ke kan motar.
Direba zai iya aiki da motarsa ko da kuwa wannan fitila na kunne amma kuma ya san da sanin cewa ba shi da kariyar da za a iya samu daga fasahar.
Za a iya gano matsalar ‘ABS’ ta hanyar yiwa motar gwajin na’ura maikwakwalwa. Ana amfani ne da wata na’ura da ake kira ‘scan tool’.  Ta wannan hanya kuma za a iya kashe fitilar bayan an gyara matsalar.

6.     MANUNIN KARANCIN ISKA A TAYA (LOW TIRE WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa



Wannan fitila na kamawa ne idan iska a daya ko sama da daya daga cikin tayoyin mota suka gaza wata ka’idar yawa.
Tafiya da tayoyi marasa isassun iska na da illa. Yin hakan ka iya jawo saurin sudewar taya da rashin dadin tafiya da karuwar shan mai da ma wasu matsalolin.

7.     MANUNIN BAIWA INJI KULAWA (CHECK ENGINE LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa




Wannan fitila na nuna cewa akwai wata matsala tattare da injin mota ko giyabos (gearbox) ko kuma ma wani abu daban da na’ura mai kwakwalwar motar (Electronic Control Module, ECM ) ta gano sannan kuma ta ajiye a kwakwalwarta.
Za a iya gano matsalar ne ta hanyar jona wata na’ura da ake kira ‘scan tool’ wadda za ta karanto matsalar da ECM din ta ajiye sannan kuma ta nuna a fuskarta (fuskar scan tool din) domin karantawa.
Bayan an gano kuma an gyara matsalar da aka gano, sai a kashe fitilar ta yin amfani da ‘scan tool’ din wadda zai goge matsalar daga kwakwalwar ECM din motar.

8.     MANUNIN BAIWA MOTA KULAWA (MAINTENANCE REQUIRED WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa



Wannan fitila na nuna cewa akwai bukatar canzawa mota bakin mai (engine oil).
Idan direba ya ga wannan alama ya kamata, ko ma ya zama dole ya je a canza masa man motarsa sannan kuma ya nemi shawarar mai gyaran ko ya dace ya canza filtar bakin mai (oil filter) da filtar fetur (fuel filter) da kuma fulogai (spark plugs).
Bai kamata a ce direba ya ke jira har sai wannan fitila ta kama ba kafin ya je ya yi canjin bakinman  (wato service).

9.     MANUNIN TAKAWAR TAYOYI DAI DAI (TRACTION WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa

 
                                                   

Wannan fitila ana samunta ne kawai a motar da aka sanyawa wata fasaha da ake kira ‘Traction Control System’ (TCS).
Wannan fasaha na taimakawa wajen nunawa direba kasancewar kyakkyawan garawa ko murzawar taya akan titi.
Wannan fitila na yin fari (flashing) ne idan tana aiki dai dai. A duk lokacin da tayoyin mota suka kasance basa murzawa dai dai to wannan fitila za ta fara fari (flashing) a inda a ke son direba ya rage gudu domin samun cikakkyiyar murzawar tayoyin akan titi.
Kasancewar wannan fitila a kunne ba tare da yin fari ba na nuna cewa akwai matsala.
Hanyar da za a iya gano wannan matsalar shine ta yin amfani da ‘scan tool’ kamar yadda aka yi bayani a sama.

10.MANUNIN DAIDAITON MOTA (VEHICLE STABILITY WARNING LIGHT)
Wannan fitila na da alama kamar yadda aka nuna a kasa


                                  


Wannan fitila ana samunta ne kawai akan motar da aka sanyawa wata fasaha da ake kira ‘Vehicle Stability Control’ (VSC). Wannan fitila na yin fari (flashing) ne idan tana aiki dai dai.
Kasancewar wannan fitila a kunne ba tare da yin fari ba na nuna cewa akwai matsala.
Hanyar da za a iya gano wannan matsalar shine ta yin amfani da ‘scan tool’ kamar yadda aka yi bayani a sama.
Wannan shine dan takaitaccen bayanin da za mu yi.




                                                                                                                                                                                                                                                                                                                            

No comments:

Post a Comment