Sunday, November 25, 2012

COMPUTERS A MOTONCIMU: YA SUKE?

Computer na da matukar amfani a duniyarmu ta yau. A yau amfani da Computer ya wuce wurin rubuce rubuce da lissafe lissafe da kalle kalle da koyar da ilmi da dai sauran ayyuka da muka fi sanin na’urar da aikatawa.

Abin da yawancin mutane basu sani ba a yau shine; a na amfani da Computer a motocin da muke hawa domin zirga zirgarmu ta yau da kullum. Kusan duk motar da ka gani a wannan zamani ta dogara ne da wani nau’i na Computer wajen gudanarwar ta. Akan yi amfani da wannan na’ura a motocin ne ta hanyoyi da yawa kamar yadda bayanin su ke tafe

Na’ura mai kwakwalwa da ke aiki a jikin mota


Wadannan  Computer na aiki ne domin tabbatar da aikin mota ba tare da wata matsala ba, da kuma tabbatar da tsaron direba, da ma sauran mutanen da ke cikin motar, tare da tsare muhalli daga gurbata. Cikin irin wadannan na’urori akwai masu sarrafa inji da masu sarrafa kofofin mota da hasken wuta da makullai da masu sarrafa gudun mota da masu sarrafa bangaren lantarkin mota da masu sarrafa aikin birki da dai sauransu.

Mafi mahimmanci cikin na’urori da ke jikin mota itace wacce ke sarrafa aikin injin motar. Wannan na’ura ta kunshi abinda ake kira ‘Engine Control Unit’ ko kuma ‘ECU’ a takaice, wadda yake shine kamar ‘Micro Processor ‘ a irin na’ura maikwakwalwa da muka fi sani. Sannan kuma akwai sauran makarrabai da ke karbo sakonni daga sassa-sassan mota wadanda sune kamar ‘Input Devices’ a Computer da muka saba da ita. Akwai kuma masu isarwa ko kuma aiwatar da sako wadanda su ne kamar ‘Output Devices’.

Foton ECU


Masansana ko kuma ‘Sensors’ a turance


Masansana sune bangarorin da suke karbo sako daga jikin mota domin aikawa zuwa kwakwalwar computer ta motar wato ‘ECU’. Misalan masansana sune: abin da ke sansano yanayin zafin inji da abin da ke sansano yanayin iskar da ke zuwa cikin inji da abin da ke sansano yanayin taka totir (throttle pedal) da direba ke yi da abin da ke sansano yanayin zafin ruwa da ke sanyaya mota da dai sauransu. masansana sune kamar ido da hanci ga injin mota.

Daya daga cikin hanyoyin da za ka gano cewa wani daga cikin masansanan motarka baya aiki shine ta kamawar wata ja ko rawayan wuta a ‘Dashboard’ din motarka. Ana kiran wannan wuta Malfunction Indicator Lamp a turance. A wata motar kuma za ka ga wani rubutu ne 'CHECK' ya kama.

kwakwalwa ko ‘ECU’


‘ECU’ ne ke karbar sakonni daga masansana ya sarrafa sakonnin, sannan ya aika da bayanin da ya dace ga bangaren da ya kamata. Alal misali, idan abin da ke sansano yanayin zafin inji ya aiko da sako cewa injin mota na da wani nau’i na zafi, ‘ECU’ zai aika da sako izuwa abin da ke fesa mai cikin inji domin ya fesa yanayin man da ya dace da wannan nau’in zafin. Wani misalin kuma shine, idan abin da ke sansano yanayin yadda direba ya taka totir ya aiko da sako izuwa ga ‘ECU’ akan cewa direba ya taka totir din sosai to ‘ECU’ din zai aika da sako izuwa ga abin da ke fesa mai da sauran wuraren da suka kamata domin bada mai da karfin wutar lantarki da ya kamata ga injin motar. Aikin wannan na’ura kan sanya injin mota ya yi aiki sosai ba tare da wata matsalaba.

Aikin Computer ga yadda injin mota ke aiki na da matukar mahimmanci. Ta na taimakawa sosai wajen rage shan mai a mota da kuma kare muhalli daga gurbata, ta hanyar rage yawan hayakin da mota ka iya fitarwa.

ECU a jikin mota


Na’ura mai kwakwalwa da ake aiki da ita don gyaran mota


Shigo da Computer cikin  mota ya sanya dole ake amfani da ita na’urar wurin gyaran motar. A yanzu akan yi amfani da Computer wurin gano matsala a mota, kai, wani lokacin ma harda a wurin gyaran motar. Kyera ita motar ko, a yanzu ba ya yiwu dole sai da injina da na’ura mai kwakwalwar ke sarrafawa.

Akwai motoci da dama a wannan zamani wadanda baya yiwuwa a gano mai ke damunsu sai an yi amfani da Computer. Wannan ke nuna cewa akwai alamun kanikanci nan gaba zai gagari da yawa daga cikin kanikawanmu na yau, sai dai in har sun nemi ilmin Computer.

Ana amfani da wata na’ura da ake kira ‘OBD Machine’ wato ‘Onboard Diagnostic Machine’ wadda akan jona a wani bangare na mota sannan a jona ita na’urar a jikin na’ura maikwakwalwa. Ita na’urar za ta gano matsalar da ke damun mota sannan ta fito da abin da ta gano a fuska ko kuma ‘screen’ din na’ura mai kwakwalwar da aka yi amfani da ita.

Na’ura mai kwakwalwa da ake amfani da ita don ganowa da kuma sarrafa mota akan hanya


Wani amfani kuma da za a iya yi da Computer a mota shine wurin sarrafa motar daga nesa, ma’ana sarrafa ita motar ba tare da mutum yana cikinta ba. Wannan fasaha kan ba ma mutum damar sanin yadda wani ke sarrafa motarsa daga wata uwa duniya. Ta yin amfani da wannan fasaha mutum zai iya gano wurin da wata mota da aka sata ta ke inhar motar na dauke da na’urar da mu ke magana akai. Kuma za a iya amfani da wannan fasaha wajen kashe injin motar ko kum kulle kofofinta ko kum kunna amsa kuwar tsaron motar. Wannan na’ura kuma kan taimakama mutum sanin wurin da motarsa ta ke daga wata uwaduniya.

Akan yi amfani da wata fasaha da ake kira GPS wajen cinma wannan buri. Ana amfani da wata na’ura ne da akan makala a jikin mota wadda ita na’urar kan aika da sako ga wata Computer wadda ita kuma kan shigar da sakon cikin yanar gizo ta inda shi kuma wanda ke son yin wani abu ga motar zai shiga yanar gizon ta yin amfanida na’urarsa mai kwakwalwa wajen cimma burinsa.
Karshen wannan makala kenan. Da fatan za ta anfanar.
Idan akwai tambaya sai a rubuta a akwatin 'comment' da ke a kasan wannan makala.

No comments:

Post a Comment